Sojojin Amirka za su zauna a Afghanistan | NRS-Import | DW | 01.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Sojojin Amirka za su zauna a Afghanistan

Amirka da Afghanistan sun sanya hannu a kan yarjejeniyar tsaro da ta ba da damar ci gaba da zaman sojojin Amirka a Afghanistan dɗn bayan kammala janyewar dakarun ƙasashen waje a karshen wannan shekara.

Sabuwar yarjejeniyar da mai bai wa shugaban ƙasar Afghanistan shawara a kan al'amuran tsaro Hanif Atmar da kuma jakadan Amirka a kasar James Cunningham suka sanyawa hannu, ta amince da ci gaba da kasancewar aƙallah dakarun Amirka 10,000 a Afghanistan din. A baya dai tsohon shugaban ƙasar Hamid Karzai ya ƙi amincewa ya ƙara rattaba hannu a kan wannan yarjejeniya da Amirka yana mai cewar ya gaji da zaman sojojin kasashen ketare a kasarsa. Da yawa daga cikin kasashen da ke cikin Ƙungiyar tsaro ta NATO da sojojinsu ke ƙasara dai sun janye dakarunsu daga Afghanistan ɗin. A karshen wannan shekara da muke ciki ta 2014 ne dai ake sa ran kammala janyewar baki ɗayan dakarun ƙasa da ƙasa daga Afghanistan ɗin.

MAawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane