Sojojin Amirka sun kai sabon hari kan IS a Iraki | Labarai | DW | 26.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Amirka sun kai sabon hari kan IS a Iraki

Sojojin saman Amirka da ke jagorantar kawancen yaki da mayakan IS da ke ikirarin Jihadi, sun kai farmaki kan sansanoninsu da ke Tikrit.

Sojojin kawancen yaki da mayakan kungiyar IS masu da'awar kafa daular Islama, sun sake kai farmaki kan sansanonin masu ikirarin jihadin a Iraki. Kakakin ma'aikatar tsaro a birnin Bagadaza ya ce jiragen saman yakin karkashin jagorancin Amirka sun kuma samu tallafi daga sojojin Iraki. A ranar Laraba ma Amirka ta kai hare-hare a birnin Tikrit da ke zama mahaifar tsohon shugaban Iraki Saddam Hussein. Tun a cikin watan Yunin bara mayakan IS suka mamaye birnin na Tikrit, kuma tun kimanin makonni hudu ke nan sojojin Iraki ke kokarin karbe iko da birnin.