Sojojin Amirka sun kaddamar da farmaki a Somaliya | Labarai | DW | 02.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Amirka sun kaddamar da farmaki a Somaliya

Amirka ta kaddamar da wani farmaki kan mayakan kungiyar al-Shabaab da ke kasar Somaliya

Ma'aikatar tsaron Amirka ta Pentagon ta tabbatar da cewa, a wannan Litinin da ta gabata sojojin kasar sun kaddamar da wani farmaki a cikin Somaliya, kan mayakan al-Shebaab.

Babu karin bayani bisa halin da ake ciki, amma haka ya biyo bayan wani hari da 'yan al-Shebaab da ke da alaka da al-Qaeda suka kai kan wani sansanin jami'an tsaro.

Cikin watannin da suka gabata dakarun kasar ta Somaliya da tallafin na kasashen Afirka sun kwace mafi yawan yankunan da suka rage a hannun al-Shebaab mai kaifin kishin addinin Islama.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu