Sojojin Aljeriya sun hallaka tsageru shida yayin ba ta kashi | Labarai | DW | 21.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Aljeriya sun hallaka tsageru shida yayin ba ta kashi

Sojojin Aljeriya sun hallaka tsageru shida yayin ba ta kashi kusa da iyakar kasar da Tunisiya da ake samun tashe-tashen hankula.

Sojojin Aljeriya sun hallaka mayakan jihadi shida cikin yankin kasar mai iyaka da kasar Tunisiya. Wata sanarwar ma'aikatar tsaro ta ce an hallaka tsagerun masu kaifin kishin Islama yayin musanyar wuta.

Mahukuntan sun karfafa tsaro saboda yaduwar ayyukan tsageru masu dauke da makamai.

Kasar ta Aljeriya ta fuskanci yakin basasa tsakanin dakarun gwamnati da tsageru masu kishin Islama cikin shekarun 1990, abin da ya yi sanadiyyar hallaka kimanin mutane 200,000. Duk da yarjejeniyar zaman lafiya gami da shirin sasantawa ana samun tashe-tashen hankula a yankunan tsakiya da gabashin kasar ta Aljeriya.