1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun yi juyin mulki a Thailand

May 22, 2014

Sanarwar sojojin a birnin Bangkok, na nuna cewar hakance mafita ga rigingimun siyasar da ya ki ci ya ki cinyewa tsawon lokaci, wanda ya haddasa asarar rayuka.

https://p.dw.com/p/1C4en
Thailand Armee Sicherheit Kriegsrecht
Hoto: REUTERS

Hafsan soji a Thailand Janar Prayuth Chan-ocha ya sanar da cewar, rundunar kasar ta karbe madafan iko sakamakon gazawar yunkurinsa na sasanta 'yan siyasar da ke adawa da juna. Jagoran rundunar sojin wanda ya sanar da kifar da mulkin cikin jawabinsa ta gidan talabijin, ya ce matakin ya zamanto wajibi domin kauce wa karin asarar rayuka da rigingimu da kuma lalata gine ginen gwamnati, kamar yadda kasar ta tsinci kanta cikin watanni da suka gabata. Kifar da mulkin dai ya kawo karshen tattaunawar sulhu da ya shiga rana ta biyu a wannan Alhamis, da ke gudana a harabar club din rundunar ta soji a birnin na Bangkok, inda hafsan sojin tun a jiya ya fara tattaunawa da wakilan sassan da ke adawa da juna, domin samar da mafita a rikicin siyasar kasar ta Thailand daya jima cikin yamutsi.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Usman Shehu Usman