Sojoji sun sa inda ′yan matan Chibok suke | Labarai | DW | 27.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojoji sun sa inda 'yan matan Chibok suke

Sojojin Najeriya suka ce sun san inda aka boye 'yan matan 'yan makaranta da aka sace a kwanakin baya a Chibok da ke jihar Borno.

Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa ta san inda aka boye 'yan mata 'yan makaranta sama da 200 da aka sace a makarantar Chibok ta jihar Borno. Sai dai kuma ba ta yi kokarin kubutar da su ba sakamakon barazanar da yunkurin ke da shi da rayukansu. Babban hapsan hapsoshin sojojin Najeriya Air Marshal Alex Badeh ya ce tsoro ka da a kakkashesu ne ya hana dakarunsa yin amfani da karfi domin cetosu.

'Yan Kungiyar da aka fi sani da suna Boko Haram ne suka sace wadannan 'yan mata a wata makaranta da ke garin Chibok a jihar Borno da ke arewacin kasar ta Najeriya. Ana hasashen cewa an boyesu ne a dajin Sambisa da ke kan iyakar tarayyar Najeriya da kamaru da Chadi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Usman Shehu Usman