Sojoji sun kashe 'yan gudun hijira a Kwango
September 16, 2017Talla
Lamarin ya faru ne a yayinda 'yan gudun hijira da masu neman mafakar siyasa a kasar Kwango, ke bore kan yadda ake tilastawa wasu 'yan uwansu ficewa daga kasar. Jakadan Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a kasar, ya ce akwai mutane 117 da hatsanioyar ya jikkata sannan an kashe guda daga cikin jami'an tsaron kasar.
A yanzu dai tuni jiragen masu saukar ungulu suka wuce da 'yan gudun hijira da suka samu munanan raunuka zuwa asibiti. Amma babu wani karin bayani daga bangaren rundunar sojin kasar, sai dai gwamnati ta umarci gudanar da bincike kan al'amarin.