Sojoji sun kashe wani a filin jirage | Labarai | DW | 18.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojoji sun kashe wani a filin jirage

Hankali ya tashi a filin tashi da saukar jirage na Orly a Faransa, bayan kashe wani da sojin kasar suka yi a wannan Asabar.

Frankreich Flughafen Paris Orly | evakuierte Passagiere (Reuters/B. Tessier)

Fasinjoji a filin jirgin Orly na Faransa

Dakarun tsaro a filin tashi da saukar jirage na Orly a Faransa, sun halaka wani mutum da hantsin wannan Asabar lokacin da ya yi yunkurin kwace makamin wani jami'in soji, abin da ya tayar da hankali jama'a dama rufe filin jirgin. Jami'ai sun ce an tsaurara tsaro a filin jirgin don gudun abin da ka je ya zo.

Dama dai kasar ta Faransa na zaman ko ta kwana, saboda tsammanin iya fuskantar hare-haren ta'addanci na masu gwagwarmaya da makamai. A ranar 23 ga watan gobe ne dai kasar za ta zabi sabon Shugaban ta, inda batun tsaro ke kan gaba cikin abubuwan da 'yan kasar za su la'akari da shi wajen zaben dan takara.

Kasar, ta yi asarar rayuka sama da 230 daga watan Janairun shekara ta 2015 zuwa yau sakamakon hare-hare na ta'addanci.