Sojoji sun gama da kungiyar I S a Iraki | Labarai | DW | 17.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojoji sun gama da kungiyar I S a Iraki

Dakarun gwamnatin Iraki da hadin gwiwar sojojinj Amirka, sun yi nasarar kwace garin Rawah tare da kakkabe kungiyar I S da ke samun mafaka a tunga ta karshe da suke iko da shi a fadin kasar.

Ma'aikatar tsaro a Iraki ta ce nasarar kwace mafakar mayakan, ya biyo bayan ba ta kashi tsakanin sojoji da mayakan na kusan sao'i biyar a garin Rawah, garin da ke da tazarar kilomita 275 da birnin Bagadaza.

Ana ganin nasarar dakarun a matsayin alamun karya lagon kungiyar I S, bayan da kungiyar ke rike da iko da yankuna masu yawa a arewacin Iraki sama da shekaru uku. A shekara ta 2014 ne mayakan suka karbe iko da wasu yankunan kasar ciki har da birnin Mosul dake zama birni na biyu mafi girma a Iraki.