Sojoji sun dakile hari a Kamaru | Labarai | DW | 15.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojoji sun dakile hari a Kamaru

Wasu 'yan bindiga da ake zargi 'yan awaren masu rajin kafa yankin Ingilishi zalla sun kai hari a kauyen Dadi da ke kudu maso yammcin kasar. Sai dai dakarun gwamnati sun yi nasarar dakile harin.

Kawo yanzu babu wadan da suka fito fili suka dau alhakin harin, amma kafofin yada labaran kasar Kamarun sun ruwaito cewa maharan sun fito ne daga wata kasa dake mokata da Kamaru. Wasu rahotanni sun ce an samu bindigogi masu yawa da wayoyin salula da rigunan "T-Shirt" mai dauke da rubutun "Dakarun tsaron yankin Ambazoniya."

'Yan aware a Kmaru sun ayyana yankin Ambazoniya a mastayin yankin da suke son kafawa mai cin gashin kai, abin da ya haddasa mutuwar mutane akalla 20 zuwa 40 a jerin zanga-zanga da aka fara tun watan Nuwamban shekara ta 2016.