Sojoji na bude wuta a tungar IS a Siriya | Labarai | DW | 10.02.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojoji na bude wuta a tungar IS a Siriya

Kawancen mayakan kurdawan SDF a Siriya da ke samun tallafin dakarun Amirka sun ce wannan mataki shi ne na karshe da zai ba su damar kwace yankunan da ke hannun mayakan IS.

Dakarun Siriya da ke samun goyoyn bayan sojojin Amirka sun kaddamar da bude wuta mai tsanani kan mayakan IS a yunkurinsu na dannawa tungarsu ta karshe.Tun shekara ta 2014 mayakan IS ke rike da manyan yankunan Siriya da ke iyaka da kasar Iraki, sai dai a baya-bayannan mayakan sun rasa iko da wasu garuruwa sakamakon taron dangi da sojojin ke yi musu babu kakkautawa, abin bda ya ba wa sojojin damar samun galaba na kwace mafi yawan yankuna daga hannun mayakan.