1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji Iraki na samun galaba a Mosul

Abdul-raheem Hassan
March 7, 2017

A wani yunkuri na raba Kungiyar IS da madafun iko a birnin Mosul na Iraki, dakarun hadin gwiwa da ke fafatawa sun yi nasarar fatattakan mayakan daga cikin wasu muhimman gine-ginen gwamnati.

https://p.dw.com/p/2YkLZ
Irak Kämpfe gegen IS in Mossul
Hoto: Reuters/G. Tomasevic

Kakakin rundunar da ke fagen daga Leutenan kanal Abdel Amir al-Mohammadawi, ya sheda wa manema labarai cewa an dau tsawon sa'a guda ana luguden wuta da mayakan, kafin daga bisani suka samu galaba a kansu. Wannan ya basu nasarar kwace babban bankin kasar da kuma babban gidan tarihin birnin da ke hannun 'yan Kungiyar ta  IS. A cewar rundunar sojin, kwace wadannan gine-gine, na zama wata dama da zai taimaka su kara nausawa cikin tungar IS da nufin tabbatar kwace cikakken iko. A tun shekara ta 2014 mayakan IS masu tsatsauran kishi addini suka karbe iko da birnin Mosul.