1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Yarjejeniyar raba madafun iko

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
August 17, 2019

Kawo yanzu akalla fararen hula uku ne dukanninsu jagororin masu bore a Sudan suka samu damar shiga cikin gwamnatin rikon kwarya.

https://p.dw.com/p/3O4Ov
Sudan Khartum Machtabgabe Militär Vertragsunterzeichnung
Hoto: Getty Images/AFP/E. Hamid

Hukumomin mulkin soja na rikon kwarya a Sudan sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar na'am game da batun rarraba mukamai tsakanin jami'an sojan kasar da masu bore na kungiyoyin fararen hula a wannan Asabar, lamarin da ya kawo karshen zaman doya da manjan da bangarorin soja da masu bore suka shafe fiye da watanni suna yi a kasar.

Tuni dai yarjejeniyar ta kai ga tabbatar da raba mukamai na majalisar zartarwar kasar ta rikon kwarya wacce daga yanzu za ta kumshi sojan da na farar hula.

Akalla kawo yanzu fararen hula uku ne dukanninsu jagororin masu boren kasar ta Sudan suka samu damar shiga cikin gwamnatin inda za su tafiyar da ayyukansu kafada da kafada da sojojin da ke jagorancin gwamnatin ta rikon kwarya.