Sojin Ukraine sun karɓe iko da Slavyansk | Labarai | DW | 05.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojin Ukraine sun karɓe iko da Slavyansk

Dakarun gwamnatin Ukaine sun kafa tutar ƙasar a birnin nan na Slavyansk wanda ke zama guda daga cikin yankunan da ke hannun 'yan awaren da ke goyon bayan Rasha.

Sojin na Ukraine dai sun kai ga yin hakan ne bayan da suka yi wani artabu na tsawon lokaci da mayaƙan 'yan awaren inda daga bisani suka ci ƙarfinsu har ma suka kai ga mamaye garin baki ɗayansa.

Mutumin da ke kiran kansa magajin garin na Slavyansk, wanda jigo ne shi a ƙungiyar ta 'yan aware ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewar mayaƙansu sun fice daga garin. A farkon watan Aprilun da ya gabata ne dai garin na Slavyansk ya faɗa cikin hannun mayaƙan 'yan awaren.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Abdourahamane Hassane