1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine za ta kai sojojin Rasha kotu

Abdul-raheem Hassan
May 14, 2022

Tawagar binciken laifuffukan yaki a Ukraine ta ce a shirye ta ke ta gurfanar da wasu mutane 41 da ake tuhuma a gaban kuliya bayan fara shari'ar farko na wani sojan Rasha a Kyiv babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/4BI8L
Ukraine Generalstaatsanwältin Iryna Venediktova beim Besuch in Borodjanka
Hoto: Zohra Bensemra/REUTERS

Babban mai shigar da kara na gwamnatin Ukraine Iryna Venediktova, ta ce ofishinta na shirya jerin laifukan yaki a kan mutane 41 da ake tuhuma. Venediktova ta ce wajibi mutanen da ake zargi su bayyana a gaban kotu kan tuhumar laifukan tada bama-bamai da kashe fararen hula da kuma zargin fyade da kwasar ganima.

A jiya Juma ne aka fara shari'ar laifukan yaki na farko tun bayan fara mamayar a birnin Kyiv da sojojin Rasha suka yi, inda ake tuhumar wani sojan Rasha mai shekaru 21 da kashe wani farar hula dan kasar Ukraine a kauyen Chupakhivka da ke arewa maso gabashin kasar.

Jami'an tsaron Ukraine sun saka wani hoton bidiyo na wanda ake zargin yana bayyana yadda ya harbe farar hular. Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun soki kasar Ukraine da buga faifan bidiyo da hotunan fursunonin yaki, wadanda a cewarsu ya sabawa yarjejeniyar Geneva.

Venediktova ta ce akwai yiwuwar wasu karin mutane biyu da ake tuhuma za su fuskanci shari'ar farko a mako mai zuwa. A baya dai Venediktova ta ce ofishinta na binciken laifukan yaki fiye da 10,700 da suka hada da mutane sama da 600 da ake zargi.