1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta halaka daruruwan 'yan Boko Haram

Gazali Abdou Tasawa
January 3, 2019

A Jamhuriyar Nijar sojojin gwamnatin kasar sun yi nasarar halaka mayakan Boko Haram kimanin 300 a wani farmaki ta kasa da ta sama da suka kaddamar kansu a yankin tabkin Chadi. 

https://p.dw.com/p/3AxCy
Nigeria Soldaten
Hoto: I. Sanogo/AFP/Getty Images

A cikin wata sanarwa da  ta fitar a jiya Laraba wadda sashen Hausa na DW ya samu kwafinta, ma'aikatar tsaron kasar Nijar ta ce baya ga mayakan na Boko Haram sama da 200 da jiragen yakin sama na kasar suka kashe, suma sojojin da ke kasa sun yi nasarar halaka mayakan na Boko Haram 87 kana suka lalata kwale-kwale guda takwas. 

Kazalika sun karbo motoci uku da manyan bindigogi da suka hada da masu aman harsasai guda biyu da na harba rakoki guda biyu da kuma harsasai sama da 2000 da wayoyin salula takwas da kuma tarin miyagun kwayoyi. 

Ma'aikatar tsaron kasar ta Nijar ta ce babu asara rai ko ta dukiya da aka samun daga bangaran sojojin na Nijar a cikin wannan farmaki wanda suka kaddamar tun a ranar 28 ga watan Disamban da ya gabata a yankin gabar kogin Komadougou na kan iyaka da Najeriya da kuma a kananan tsibirrai da ke a yankin tabkin Chadi da ke zama mabuyar mayakan na Boko Haram.