1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An halaka mayakan 'yan awaren Kamaru

Gazali Abdou Tasawa
November 14, 2018

A kasar Kamaru mayakan 'yan awaren Ambazoniya akalla 25 suka kwanta dama a cikin wani fada da sojojin gwamnati a kusa da birnin Nkambe na yankin Arewa maso yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/38EcC
Kamerun Mora Armee Soldaten Anti Boko Haram 07/2014
Hoto: Reinnier Kaze/AFP/Getty Images

Wata majiyar tsaro a birnin Yaounde ta gabatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP wasu hotunan na gawarwaki kimanin 10 na 'yan awaren da aka kashe a cikin fadan. Sojojin gwamnatin kasar ta Kamaru sun ce a wannan gumurzu wanda ya gudana a cikin makarantar kauyen Mayo Binka inda mayakan 'yan awaren suka ja daga sun yi nasarar kame tarin makamai akasarinsu bindigogin farauta. 

Babban jami'in kula da harkokin farfaganda na 'yan awaren kasar ta Kamaru Mark Bareta ya tabbatar da afkuwar wannan fada a wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta inda ya ce mayakansu da dama sun halaka amma kuma ya ce sun kashe sojojin gwamnati da dama. Sai dai rundunar sojojin Kamarun ta ce babu sojinta daya da ya mutu a cikin wannan fada.