Sojin Chadi sun karbe Gamboru daga ikon Boko Haram | Labarai | DW | 03.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojin Chadi sun karbe Gamboru daga ikon Boko Haram

Sojojin Chadi sun kwace garin Gamboru dake jihar Borno a Najeriya

Rahotannin dake fitowa daga Gamborun jihar Bornon Najeriya, na cewa sojojin Chadi sun yi bata-kashi da mayakan Boko Haram a yau Talata, inda suka karbe garin daga hannun kungiyar.

Arangamar sojojin na Chadi da mayakan na Boko Haram dai har ila yau na zuwa ne bayan jerin lugudan wuta da dakarun suke yi kan 'yan kungiyar ta sama, a 'yan kwanankin nan tsakanin Najeriya da kasar Kamaru.

Shelkwatar sojin Chadin ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa, suna ci gaba da fatattakar 'yan kungiyar ta Boko Haram a karawar ta yau.

A kwanakin da suka gabata ma sojojin na Chadi sun kwato garin Malumfatori daga hannun 'yan kungiyar ta Boko Haram duk dai jihar ta Borno.

A halin yanzu dai, dakaru dubu biyu da 500 ne kasar Chadi ta bayar don fuskantar Boko Haram din dake kaddamar da hare-hare arewa maso gabashin Najeriya dama wani sashen kasar Kamaru.