Sojin Amirka da ya tsere ya rasu | Labarai | DW | 21.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojin Amirka da ya tsere ya rasu

Rahotanni daga Koriya ta Arewa na cewa James Joseph Dresnok sojin kasar Amirkar nan wanda ya tsere zuwa Koriya ta Arewa shekaru 50 da suka gabata ya rasu. 

Rahotanni daga Koriya ta Arewa na cewa James Joseph Dresnok sojin kasar Amirka  wanda ya tsere zuwa Koriya ta Arewa  shekaru 50 da suka gabata ya rasu. 

Iyalan mamacin ne suka tabbatar da wannan labari inda suka ce ya rasu ne tun a bara, bayan ya sake jaddada mubaya'arsa ga Kim Jong-Un a lokacin da yake kan gadonsa na mutuwa. James Josef wanda ya rasu yana da shekaru 74 na daga cikin rukunin wasu sojojin kasar ta Amirka da suka gudu zuwa Koriya ta Arewa  a shekara ta 1962 bayan kammala yakin da ya kai ga raba hadaddiyar Koriyar zuwa kasa biyu a shekara ta 1950 zuwa 1953. 

A wata hira da suka yi a cikin wani faifayin bidiyo da aka wallafa a shafin yanar gizo na Uriminzokkiri na Koriya ta Arewar 'ya'yan marigayin wato Ted da James sun yi hannunka mai sanda ga kasar Amirka a game da neman yakin da ta ke yi da Koriya ta Arewa inda suka ce da ta san hakikanin karfin sojin Koriya ta Arewar ta ke da shi a yanzu to kuwa da ba za ta kuskura ta nemi yaki da ita ba.