Sojan Saudiyya da mayakan Houthi na gwabza fada | Labarai | DW | 31.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojan Saudiyya da mayakan Houthi na gwabza fada

Mahukuntan na kasar ta Saudiyya karkashin sojan kasar sun zage dantse wajen ganin bayan mayakan na Houthi da ke samun goyon bayan kasar Iran.

Dakarun sojan kasar Saudiyya da mayakan Houthi na kasar Yemen sun yi barin wuta da makaman atilare da rokoki a lardina da dama a yau Talata a kan iyakar kasashen biyu kamar yadda wasu mazauna yankunan da wasu kabilu suka bayyana wa kamfanin dillancin labaran Reuters.

Mazauna yankin sun bayyana cewa jirgin sama mai saukar ungulu na shawagi a yankin da suke inda ake yakin da ya zama mafi muni cikin kwanaki shida da kasar ta Saudiyya ta yi tana lugudan wuta kan mayakan Houthi da ke samun goyon bayan kasar Iran dan karya lagon wadannan mayakan sakai a kasar ta Yemen.