1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojan kundunbala na son kare birnin Kudus

Yusuf Bala Nayaya
December 12, 2017

Sojan Iran na (IRCG) Janar Qasem Soleimani ya bayyana cewa a shirye yake na bada gudunmawarsa ga 'yan fafutikar kare hakkin Falasdinawa.

https://p.dw.com/p/2pBW2
Iran Wochengalerie KW 14
Ali Khamenei na karbar gaisuwar Janar Qasem Soleimani Hoto: Isna

Bayan da ake ci gaba da samun zanga-zanga ta adawa da shirin Shugaba Donald Trump na Amirka da ya ayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra'ila wani babban kwamanda daga sojan kundunbalar kasar Iran na  (IRCG) ya bayyana cewa a shirye yake na bada gudunmawarsa ga 'yan fafutikar kare hakkin Falasdinawa.

Janar Qasem Soleimani ya bayyana wannan aniya ce ga kwamandan dakarun sojan Falasdinawa bangaren Hamas al-Qassam Brigades da suke da iko da yankin Hamas. Shafin intanet na sojan kundunbalar na Iran IRCG ya ce kwamandojin sun yi wannan tattaunawa ne a jiya Litinin kamar yadda kafar yada labaran Sepahnews ta bada labarin.

Janar Soleimani ya ce yankin zai ci gaba da fafutika ta ganin an kare wannan birni da ke zama mai tsarki na uku ga mabiya addinin Islama da ma mabiyan addinin na Yahudawa da Kirista.