1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alkalan Tunisiya sun yi barazanar fadada yajin aiki

Suleiman Babayo ATB
June 9, 2022

Kungiyar Kwadagon Tunisiya ta zargin gwamnati da neman kassara harkokinta yayin da alkalai ke ci gaba da yajin aiki.

https://p.dw.com/p/4CTRE
Tunesien | Proteste in Rades
Hoto: Chokri Mahjoub/Zuma/picture alliance

Babbar kungiyar kwadago ta kasar Tunisiya mai karfin fada aji, ta  UGTT, ta zargi hukumomin kasar da suka kungiyar a gaba bayan da kaurace wa shiga tattaunawar samar da sabon kundin tsarin mulki. A watan da ya gabta Shugaba Kais Saied ya kira taron samar da sabon kundin tsarin mulkin.

Shugaban kungiyar kwadagon Noureddine Taboubi bai yi karin haske ba kan batun, amma majiyoyi na kusa da kungiyar kwadagon sun ce shugaban kasar yana neman amfani da bangare sharia wajen musguna wa 'yan kwadagon, kamar yadda ya yi wajen koren alkalai da dama daga bakin aiki.

Alkalan kasar Tunisiya sun yi barazanar fadada yajin aikin da suke yi zuwa mako na biyu muddun shugaban kasar Kais Saied ya ki doke ayar dokar da ya kafa inda ya kori alkalai da dama daga bakin aiki, kamar yadda shugaban kungiyar alkalan ya tabbatar.

A makon jiya shugaban kasar ya sallami alkalai 57 da ya zarga da cin hanci da kuma ta'addanci, cajin da kungiyar alkalan ta yi twasi da su a matsayin yarfe na siyasa.