Siyasar Nijar na fiskantar kalubale daga matasa | Siyasa | DW | 03.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Siyasar Nijar na fiskantar kalubale daga matasa

A Jamhuriyar Nijar wasu kungiyoyin fararen hula na matasa sun kulla wani sabon kawance da zummar kawo guguwar sauyi a fagen dimukradiyya da ma 'yan siyasar kasar mai suna "Mouvement Pour la Révolution Démocratique".

Sabon kawancen na mai hankorin kawo wani sauyi a fagen dimukradiyya na shirin fito na fito da 'yan siyasar kasar ya Allah wadanda suke mulki a yanzu ko kuwa ma wadanda su ke cikin adawa biyo bayan lurar da suka ce sunyi na rashin samun wani gagarumin sauyi a rayuwar talakawan kasar musamman ma ga matasa bayan shafe sama da shekaru 25 ana tafiyar da mulkin dimukradiyya.

Kungiyoyin na zargin daukacin 'yan siyasar kasar ne da arzirta kansu da dukiyar kasa da zamba cikin aminci har ma da ci da gumin talakawa da sunan dimukradiyya alhali kuwa dokokin kasa sun ce mulkin a na yinsa don jama'a da cigaban jama'a.

Malam Abdoulmoumouni Ousmane shi ne madugun kungiyoyin na Révolution démocratique na mai ra'ayin cewa jam'iyyun siyasar ta Nijar gaba dayansu na mutane ne da ba su yi wa talakawa aiki.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da wasu matasan ke hada kai don kafa wani gungu da zummar kawo sauyi a fagen dimukradiyya, sai dai mafi akasari kawancen kan kai ga gurfana ga akida da ma manufofin wasu 'yan siyasa wanda wasu lokutan batun manufarsu ta farko kan sulalewa ko kuma ya zama irin zance na 'yan matan amarya kawai.To amma sai dai shugaban kwamitin hadin gwiwar kungiyoyin matasan ya ce tafiyar ta wannan karon ta banbanta da wadanda suka sha shudewa.

Allah ya albarkaci jamhuriyar Nijar da dimbin arziki na ma'adanai ga yawan matasa akalla sama da kashi 50% sai dai galibinsu na fuskantar matsalolin rayuwa na yau da kullum sakamakon fatara da talauci da rashin aikin yi da wadatacen ilim inji rukunin kungiyoyin saboda hakan lokaci ya yi da ya kamata a ce sun tashi don hada kai waje daya a dimukradiyance don debewa kan su takaici a cewar sanarwar karshen taron sabon kawancen na Mouvement pour la révolution démocratique. 

Sauti da bidiyo akan labarin