Siti Binti Saad, fitacciyar mawakiyar Taarab a Zanzibar | Tushen Afirka: mutanen da suka taka rawa a tarihin Afirka | DW | 28.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Tushen Afirka

Siti Binti Saad, fitacciyar mawakiyar Taarab a Zanzibar

Siti Binti Saad fitacciyar mawakiyar Taarab ce kana ta yi fice wajen yin fafutuka musamman ga mata a gabashin Afirka.

Yaushe ne Siti Binti ta rayu?

An haifi Siti Binti a shekarar 1880 a kauyen Fumba na yankin Zanzibar, wanda wani bangare ne na kasar Tanzaniya. Mahaifanta masu karamin karfi ne. Siti ta yi talla kan titunan kauyensu kafin daga bisani ta yi kaura zuwa Zanzibar a shekarar 1911. A can ne ta fara aiki da wasu mawaka, inda daga bisani ta zama shahararriyar mawakiya ta Taarab. Ta yi ta yin wannan sana'a ce har lokacin da ta tsufa. Siti Binti ta rasu a shekarar 1950.

 

Wane abu ne ya sa Siti Binti Saad ta yi fice?
Siti Binti ta yi fice a harkar waka ta Taarab. Allah Ya albarkaceta da murya mai kyau, wannan ya sanya an gayyaceta don yin wasa a fadar Sultan. Baya ga manyan mutane da Siti kan ziyarta don yi musu waka, ta kuma yi wa sauran rukunin al'umma waka kuma gidanta ya kasance wani waje da a kan hadu don musayar ra'ayi da kuma muhawara kan batutuwa da dama.

 

Shin da wane matsayi Siti Binti Saad ta fara?

Kafin ta fara waka, maza masu ilimi ne ke yin wakar Taarab, kuma a kan yi ta da harshen Larabci wanda shi ne harshen da ake amfani da shi a Zanzibar, musamman ma ga wanda suke da ilimi. Siti Binti ita ce mace ta farko wadda ba ta da zurfin ilimi da ta yi fice a tsarin waka na Taarab kuma ta sanya wannan tsari ya yi suna kasancewar ta rika yin amfani da harshen Swahili wajen yin wakar. Wannan ne ya sanya wani kamfanin Birtaniya da ke yin na'urar garmaho, ya kaita birnin Bombay na kasar Indiya don nadar muryarta. Wadda hakan ya sanya ta kasance 'yar gabashin Afirka ta farko da aka nadi muryarta don amfani da ita a matsayin talla.

 

A dubi bidiyo 01:41

Siti Binti Saad, fitacciyar mawakiyar Taarab a Zanzibar

Shin me wakokin Siti Binti Saad suka mai da hankali a kai?

Da yake ta kan yawaita sauraron jama'a, wakokin Siti Binti sun mai da hankali ne kan irin abubuwan da ke damun al'umma. Wakokinta sun yi magana a kan rayuwa ta yau da kullum a Zanzibar, sannan sun kunshi yin kakkausar suka da nuna rashin amincewa da danniyar da ake yi wa mutane da cin hanci da kuma yadda maza ke cin zarafin mata. Baya ga haka, wakokin sun tabo irin raunin da tsarin shari'a a kasar ke da shi.

 

Su waye Siti Binti ta zaburar?
Siti Binti ta zaburar da mawaka da dama kana ta yi tasiri a kan aiyukansu, sannan ta bude wata hanya ta samun karuwar mata da ke yin wakoki irin na Taarab. Ita ce ta horas da Bi Kidude wadda daga bisani ta kasance fitacciyar mawakiyar Taarab. Siti Binti ta hadu da shahararren marubucin wakokin Swahili wato Shaaban Robert, wanda ya rubuta tarihin rayuwarta wato ''Wasifu wa Siti Binti Saad''. Bayan rasuwarta aka buga wannan littafi kuma ya kasance wani aiki da za a ce yana da muhimmanci idan ana magana ta dab'in Swahili, wanda ake karantarwa a makarantu. Shaaban Robert ya kira wakokin Siti Binti ''abin alfahari na gabashin Afirka'' sannan ya ce muryoyinta da aka nada ''haske ne maganin duhu''. Wata mujalla da aka yi wadda ta fi mai da hankali kan lamuran da suka shafi harkoki na mata, wadda wata kungiyar mata da ke aiki a kafafen yada labarai ke wallafawa ta sanya wa kanta suna ''Sauti ya Siti'' wato ''Muryar Siti''.

 

Wane abu ne Siti Binti Saad ta bari da za su sa a tuna da ita?

Siti Binti ta yi wakokin da yawansu ya kai 250, amma kalilan ne daga cikin wadannan wakoki ake da su a yau. Ana yawan sauraron wakokinta a kasar Tanzaniya da ma sauran wurare. Wakokin nata wani ginshiki ne na tsarin waka na Taarab. Shekarar 2017 ta kasance shekarar da aka kafa wata cibiya da aka kira "Activist Siti Bint Saad Institute". Makasudin kafa wannan cibiya shi ne adana wakokinta da kuma ciyar da al'adu da dabi'un Zanzibar.

 

Shiri na musamman "Tushen Afirka" aiki ne na hadin gwiwa tsakanin DW da Gidauniyar Gerda Henkel.

Sauti da bidiyo akan labarin