Siriya ta kori jami′an Majalisar Dinkin Duniya a kasarta | Labarai | DW | 27.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya ta kori jami'an Majalisar Dinkin Duniya a kasarta

Gwamnatin Siriya ta kori jami'an Majalisar Ɗinikin Diniya da ke kasarta

Gwamnatin ƙasar Syria ta kori wasu jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya uku daga ƙasarta a dai lokacin da mai shiga tsakani na majalisar t ke daf da ziyartar ƙasar don tattauna yiwuwar Syriyar ta tsagaita kai hare-hare kan birnin Aleppo. Wannan matakin ana ganin zai kawo tarnaƙi ga samar da tallafi a ƙasar, a lokacin kuma da ake kan buƙatar haka.

Ana dai saran ziyarar ta Staffan de Mistura mai shiga tsakanin na MDD a gobe Asabar za ta yi tasiri ga buƙatar tsagaita kai hare-hare kan Aleppo da ke arewacin ƙasar na makonni shida.