Siriya: Mutane sama da 40 sun mutu a harin ta′addanci | Labarai | DW | 29.04.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya: Mutane sama da 40 sun mutu a harin ta'addanci

A Siriya mutane 46 ne sojoji da fararan hula suka halaka a cikin wani harin ta'addanci da aka kai a yammacin jiya Talata a kasuwar birnin Afrine na arewacin kasar da ke a karkashin ikon sojojin gwamnatin kasar.

A kasar Siriya mutane 46 ne sojoji da fararan hula aka tabbatar sun halaka ya zuwa yanzu a cikin wani harin ta'addanci da aka kai a yammacin jiya Talata a kasuwar birnin Afrine na arewacin kasar da ke a karkashin ikon sojojin gwamnatin kasar. Kungiyar OSDH ta masu sa ido a yakin kasar ta Siriya ta ce an kai harin ne da wata motar dakwon man fetur da aka dana wa bam wacce ta tarwatse a cikin kasuwar inda ta halaka mutane 46 da suka hada da kananan yara 11 a yayin da wasu mutanen 50 suka jikkata. Kawo yanzu dai ba kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan hari wanda ake fargabar samun karin mutuwa a cikinsa ta la'akari da yadda wasu suka ji munanan raunika. Sai dai gwamnatin Turkiyya ta dora alhakin hari ga kungiyar mayakan Kurdawa ta YPG da kawayenta.