Siriya: IS ta yi garkuwa da mutum 700 | Labarai | DW | 19.10.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya: IS ta yi garkuwa da mutum 700

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya ce mayakan IS sun yi barazanar kashe mutum goma a kowacce rana daga cikin daruruwan da suka yi garkuwa dasu muddun ba a biya musu bukatunsu ba.

Mutune kusan dari bakwai mayakan kungiyar IS ta yi garkuwa da su a yankin Deir-al Zor da ta ke da karfin iko a kasar Siriyan. Putin ya ce wadanda aka yi garkuwa da su, sun hada da 'yan asalin kasashen Amirka da wasu daga kasashen nahiyar Turai, ya kara da cewa, IS ta gindaya wasu sharruda da ta nemi a cika mata su.

Shugaban na Rasha da kasarsa ke tallafawa gwamnatin Bashar al-Assad don ganin ta yi nasarar a yakin na Syria, bai yi karin bayani kan bukatun kungiyar ba. Kafin wannan ma dai kafar talabijin ta kasar Rashan, ta bayar da labarin yin garkuwa da mutane dari bakwai da ta ce wani jami'in soji da ya nemi a sakaya sunansa ya kwarmata.An gano yadda aka file kan mutum goma a jiya daga cikin wadanda ake garkuwa da su.