Siriya: Ghouta na fuskantar kalubale | Siyasa | DW | 01.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Siriya: Ghouta na fuskantar kalubale

Kasashen duniya sun nuna damuwarsu kan halin da ake ciki a yankin gabashin Ghouta na Siriya, tun bayan da sojojin gwamnati tare da ban hannun Rasha suka ayyana kai hari kan 'yan tawaye.

Tun bayan da sojojin gwamnatin Siriya da ke samun goyon bayan Rasha da ma kasar Iran suka ayyana kai hare-hare a yankin gabashin Ghouta kusa da Damaskus babban birnin kasar ta Siriya, al'ammura sun ci gaba da lalacewa musamman ma a fannin mace-macen fararan hulla da kuma shigar da kayayyakin agaji. Hakan ya sanya Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin duniya, ya yi zama domin tilasta tsagaita buda wuta don a samu shigar da kayayakin agaji zuwa yankin na Ghouta. Fararen hula da ke rayuwa a gabashin garin na Ghouta na cikin matsatsi, kuma da dama na fama da rashin lafiya da karancin abinci na ruwan sha.

DW.COM