Siriya: Ana kai sababbin hare-hare kan IS | Labarai | DW | 12.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya: Ana kai sababbin hare-hare kan IS

Gwamantin Siriya ta tsananta kai hare-hare a yankin al-Bu Kamal sa'o'i kalilan bayan kwace iko da wasu muhimman garuruwa da mayakan kungiyar IS suka yi a kan iyakar kasar da Iraki.

 Rahotanni sun ce hare-haren sun yi sanadin mutuwa tare da jikkata fararen hula masu yawa sakamakon luguden wuta ta sama da aka kwana ana yi. Kungiyar kare hakkin dan Adam da ke sanya idanu a yakin na Siriya wadda kuma ke da cibiya a Birtaniya, ta ce ana can ana ci gaba da musayar wuta tsakanin dakarun hadin gwiwa da kuma bangaren mayakan na IS a yankunan da ke kusa da yankin na al Bu Kamal. A ranar Alhamis ne dai kungiyar ta IS ta sake kwace gabashin lardin Dier al Zour mai arzikin man fetur.