1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan adawar Siriya sun yi Allah wadai da jawabi kan Idlib

Zulaiha Abubakar
August 31, 2018

'Yan adawa a Siriya sun yi Allah wadai da Staffan de Mistura wakilin Majalisar Dinkin Duniya bayan ya bukaci kawo karshen yan ta'addan dake yankin Idlib.

https://p.dw.com/p/346QL
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Siriya, Staffan de Mistura a wani taro da ya gudana a Astana
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Siriya, Staffan de Mistura a wani taro da ya gudana a AstanaHoto: picture-alliance/dpa/M. Tereshchenko

Da yake karin bayani Yehia Arid guda cikin wakilan 'yan adawa a tattaunawar sulhun da Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta kan rikicin na Siriya ya zargi Mistura da ingiza gwamnatin kasar Siriya ta yi amfani da makami mai guba wajen kai hari yankin na Idlib.