Siriya: An bukaci kare rayukan fararen hula | Labarai | DW | 17.01.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya: An bukaci kare rayukan fararen hula

Shugabar hukumar kare hakkin 'dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet ta bukaci kawo karshen rikici a yankin Idlib na Siriya, bayan ta bayyana takaicin yadda mahukunta suka gaza kare rayuwar fararen hula.

Bachelet ta kuma kara da yin Allah wadai da yadda bangarorin da ke rikici da juna a Siriya suke luguden wuta ta sama a yankunan da fararen hular ke zaune, a jiya Alhamis wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewar daga watan Disambar bara zuwa yanzu akalla al'ummar Siriya da yawansu ya kusan dubu dari uku da hamsin, mafiya yawansu mata da kananan yara sun tsere daga yankin na Idlib zuwa makotan yankuna a iyakokin kasar da Turkiyya inda suke rayuwa cikin ragaita.