Siri Lanka ta nemi taimako | Labarai | DW | 28.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siri Lanka ta nemi taimako

Sri Lanka ta nemi taimakon kasashen duniya bayan zabtarewar kasa da ta hallaka fiye da mutane 150

Masu aikin ceto a kasar Siri Lanka sun gano karin mutanen da suka hallaka sakamakon zabtarewar kasa da aka samu bayan kwashe kwanaki biyu ana sheka ruwan sama. Gwamnati ta tabbatar da mutuwar fiye da mutane 150 yayin da wasu fiye da 110 suka bace kuma ake ci gaba da nama.

Gwamnatin kasar ta Siri Lanka ta bukaci taimakon kasashen duniya, saboda barazanar da kimanin mutane 100,000 suke fuskanta wadanda bala'in ya shafa. Tuni wasu kasashe suka fara kai dauki.