Siri Lanka: An kama mutun 40 bayan hari | Labarai | DW | 23.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siri Lanka: An kama mutun 40 bayan hari

A ci gaba da bincike kan hare-haren ta'addanci na ranar Ista a Siri Lanka, 'yan sanda sun kama mutane 40 a daidai lokacin da adadin mutanen da suka mutu ya kai 310.

A kasar Siri Lanka adadin mutanen da suka mutu a cikin jerin hare-haren ta'addanci da aka kai a ranar Lahadi ya karu zuwa mutun 310 a wannan Talata, bayan da da dama daga cikin wadanda suka jikkata a lokacin hare-haren suka kwanta dama daga bisani. 

Mahukuntan kasar dai sun sanar da kame ya zuwa yanzu mutane 40 a ci gaba da binciken da suke kan wadannan hare-haren ta'addanci wadanda hukumar 'yan sandan kasar ke zargin wata sabuwar kungiyar masu kaifin kishin Islama ce mai suna NTJ wato National Thowheeth Jama'at ta kai su. 

Al'ummar kasar ta Siri Lanka ta yi tsit na mintoci uku a safiyar wannan Talata domin tunawa da mutanen da suka mutu a hare-haren wadanda aka kai a manya otel-otel da mujami'u a daidai lokacin da ake bikin Ista. Gwamnatin kasar ta kaddamar da zaman makoki na yini daya a wannan Talata inda shagunan sayar da barasa za su kasance a rufe a duk tsawon yinin na yau.