Simone Gbagbo za ta yi zaman gidan yari | Siyasa | DW | 10.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Simone Gbagbo za ta yi zaman gidan yari

Kotu a Cote d'Ivoire ta daure Simone Gbagbo, matar tsohon Shugaba Laurent Gbagbo shekaru 20 sakamakon hannu da aka same ta da shi a tashin hankalin na bayan zabe a kasar.

An sami Simone Gbagbo da laifin zagon kasa ga tsaron kasa bayan zaben shugaban kasa na karshen shekara ta 2010, abin da ya janyo tashin hankali a 2011 wanda kuma ya yi sanadiyar hallaka mutane 3,000. Simone ta fuskanci tuhumar tare da wasu mutane 82 da ke zaman tsofaffin jami'an gwamnati da 'yan tsohuwar jam'iyya mai mulki.

Laurent Gbagbo Anhörung Internationaler Gerichtshof in Den Haag

Laurent Gbagbo na amsa tuhuma a kotun ICC kan rikicin zaben 2010.

Kotu ta samu Simone Gbagbo 'yar shekaru 65 da haihuwa da laifi na goyon bayan mijinta Laurent Gbagbo shugaba kasa a wancan lokaci, wanda ya ki amincewa da shan kaye a zaben watan Nowamba na shekara ta 2010, wanda hukumar zabe ta tabbatar cewa tsohon Firamnista Alassane Ouattara ya lashe.

Da ya ke tsokaci kan batu, guda daga cikin lauyoyin da ke kare Ms. Gbagbo ya ce "a kan wacce hujja suka yanke wannan hukunci? Ko kadan ba a yi aiki da abin da dokokin shari'a suka tanada ba. Wannan wani abin takaici ne ga Cote d'Ivoire."

Krise in der Elfenbeinküste

Rikicin bayan zabe a Cote d'Ivoire ya hallaka mutane da dama.

A kalamansa da ke kama da maida martani ga lauyan Ms. Gbagbo, Alain Gbokola da ya jagoranci lauyoyi masu shigar da kara cewa ya yi "akwai sama da mutane dubu uku da aka kashe a Cote d'ivoire wasu da ransu ma aka konesu kurmus, dangane da haka mu a matsayinmu na wakilan gwamnati mun gamsu da wannan hukunci."

Wannan dai ba shi ne karon farko da Simone Gbagbo za ta yi zaman jarun ba domin kuwa a shekarun 1970 an daure ta saboda yadda ta ke fito na fito da gwamnatin kasar ta Cote d'Ivoire a lokacin da ke bangaren 'yan adawa.

Sauti da bidiyo akan labarin