Simone Bagbo matar tsohon shugaban Côte d′Ivoire na shirin fuskantar kotun kasa da kasa | Labarai | DW | 04.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Simone Bagbo matar tsohon shugaban Côte d'Ivoire na shirin fuskantar kotun kasa da kasa

Tun bayan da kotun kasa da kasa mai hukunta manyan laifufuka ta bada samacin kamun matar tsohon shugaba Bagbo,hankali ya karakata ga matsayinta a kotun.

default

Simone Gbagbo matar tsohon shugaban kasar Côte d'Ivoire

A wana ganawar da yayi da masu hannun da shuni a wannan Talatar,praministan Côte d'Ivoire Daniel Kablan Ducan,ya ce kawop yanzu ba a dauki wata kwakwarar shawara ba a kan matsayin matar tsohon shugaban kasar Laurent Bagbo a dangane da bukatar aikata kotun kasa da kasa da ke hukunta manyan laifufuka da ke da cibiyarta a birnin Hage. A shekara ta 2011 ne kotun ta bada samacin cafke Simone Bagbo da ake zargi da hannu a rikicin kasar da ya biyo bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar wanda kuma ya yi sanadiyar mutuwar kimanin mutane dubu 3.
A shekara ta 2011 ne hukumomin kasar suka tusa keyar mijinta a kotun ta kasa da kasa,to saidai kawo yanzu ba a yanke masa hukunci ba,a zargin da ake masa na hura wutar rikicin da ya barke a kasar.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Zainab Mohamed Abubakar