1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban: Shurun kungiyoyin addinin Islama

September 16, 2021

Wasu masanan Addinin Musulumci sun fara sukar yadda kungiyoyin addinin Islama ke dari-dari, wajen yin martani game da karbe iko da Taliban ta yi a Afghanistan da kuma halayenta.

https://p.dw.com/p/40PJc
Afghanistan Taliban
Cikin watan Agustan da ya gabata ne, mayakan Taliban suka kwace iko a AfghanistanHoto: AFP/Getty Images

Tun lokacin da Taliban suka karbi iko a kasar Afghanistan aka ci gaba da yin gum da bakuna, babu wani matakin kai tsaye da wata kasa ta dauka. Yayin da shugabanni da wakilan kungiyoyin Musulmi suka yi tsit, haka su ma kasashen yamma sun kasa samun dai-daito kan yadda za su rika tafiya da kungiyar Taliban din da ta kwace iko a Kabul, kamar yadda Milad Karimi mataimakin shugaban tsangayar koyar da addinin Islama da ke jami'ar Münster ta Jamus ya nunar.

Karin Bayani: Nasarar Taliban da masu ikirarin jihadi

Sai dai ko wane irin matsin lamba da zai fiito daga kungiyoyi da shugabannin kasashen Yamma, masana addinin Mususlumci na cewa babu abin da zai sa kungiyar Taliban ta sauya fassarar da ta yi wa wasu manufofi da suka samo asali daga cikin Alkur'ani. 'Yan kungiyar ta Taliban dai, sun dora tafiyar da alamuransu ne bisa mahimtarsu da koyarwar addinin Islama.

Afghanistan Bildungsuniversität Kabul
Tun bayan da Taliban ta karbi iko a Afghanistan, matan kasar ke cikin fargabaHoto: Bilal Guler/AA/picture alliance

A cewar Milad Karimi 'yan Taliban ba za su taba raba mulkinsu da kuma tsarin Islamar da suka fahimta ba. Babban abin da aka fi sukar Taliban kansa dai shi ne batun mata. A tsarin kungiyar mata ba su da wani aiki illa su kasance karkashin mazajensu suna biya masu bukata su raini yara su kuma kula da ayyukan cikin gida yayinda mai gida zai fita nemo abinci.

Karin Bayani: Afghanistan na cikin mawuyacin hali

Wannan kuwa yana daga cikin tsarin da masu fafutuka ke cewa abu ne da ake bi shekaru sama da 1,400 kuma yanzu zamani ya sauya. Su kuwa Taliban da ke iko a Afghanistan a yanzu a fahimtarsu Addinin Musulumci ba ya tafiya da zamani, wanda ma ke fadin haka suna ganinsa a matsayin makiyi a cewar Susanne Schröter kwararriya a sashin nazarin Addinin Islama na jami'ar Frankfurt da ke Jamus. Tuni dai wadannan matakai na yin aiki da tsarin Islamar da Taliban ta fahimta, ya samu karbuwa daga kungiyoyin Musulmai kamar Muslim Brotherhoods da kuma ta 'Yan Salafiya ko da kuwa ba sa cikin kungiyar 'yan ta'addanci ta IS.