Shugabar Mauritius za ta ajiye aiki | Labarai | DW | 09.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabar Mauritius za ta ajiye aiki

Shugabar Mauritius Ameenah Gurib-Fakim za ta sauka daga mukaminta bayan zarginta da aka yi da amfani da wasu kudade ba bisa doka ba. Shugabar ta Mauritius dai ita ce mace tilo da ta ke mulki a Afirka.

Bibi Ameenah Firdaus Gurib-Fakim (DW/S.Diehn)

Shugabar kasar Mauritius, Ameenah Firdaus Gurib-Fakim

Shugabar kasar Mauritius Ameenah Gurib-Fakim za ta sauka daga mukaminta, bayan zarginta da aka yi da wata badakalar da ta shafi kudade. Shugaba Ameenah Grib-Fakim wacce Farfesa ce, ita ce kadai shugaba mace a nahiyar Afirka a yanzu. Tana fuskantar zargi ne na amfani da wani katin cirar kudi na wata kungiya, inda ta ke biyan bukatunta da su.

A cewar firaministan kasar Pravind Jugnauth, shugabar kasar za ta sauka ne bayan bikin cikar kasar shekaru 50 da samun 'yanci wanda za a yi a ranar Litinin na makon gobe.