Shugabar Koriya ta Kudu ta mika kai ga majalisa | Labarai | DW | 29.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabar Koriya ta Kudu ta mika kai ga majalisa

Tuni wasu daga 'yan majalisa na jam'iyyar shugabar ta Saenuri suka yi mata tayi na ta sauka daga mulki ta tafi cikin mutunci.

A ranar Talatan nan ce Shugabar Koriya ta Kudu Geun-hye ta yi jawabi ga al'umma lokacin da ake ci gaba da kiraye-kiraye na ta sauka daga mulkin kasar biyo bayan badakalar cin hanci da ake zargin hannun shugabar a ciki. Shugabar dai ta amince da cewa majalisa ta dauki matakin da ya dace kan makomarta. Tuni wasu daga 'yan majalisa na jam'iyyar shugabar ta Saenuri sun mata tayi na ta sauka daga mulki ta tafi cikin mutunci, yayin da 'yan adawa ke kara matsa lamba kan kudirin dokar neman tsige shugabar.

Sau biyu ne dai shugabar ke bayyana neman afuwar al'umma sakamakon badakalar da ta hada da tsohuwar abokiya gareta, sai dai kira na ta sauka daga mulkin kasar na ci gaba da karuwa.