Shugabar gwamnatin tarayyar Jamus Angela Merkel na ci gaba da ziyararta a Isra’ila. | Labarai | DW | 30.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabar gwamnatin tarayyar Jamus Angela Merkel na ci gaba da ziyararta a Isra’ila.

A ci gaba da ziyarar da take kaiwa a kasar Isra’ila, shugabar gwamnatin tarayyar Jamus Angela Merkel ta halarci wani biki a birnin kudus, inda ta aza furanni a gidan Yad Vashim, gun juyayin yahudawa miliyan 6 nan da `yan mulkin Nazi suka halakad da su a lokacin yakin na biyu. Shugaban ta bayyana cewa, Jamus dai ta kasance rikakkiyar mai goyon bayan Isra’ilan ne tun karshen yakin duniya na biyu. Kuma za ta ci gaba da mara mata baya, musamman ma dai a lokutan da ta fi huskantar kalubale. Ita dai Merkel, ita ce farkon shugabar wata kasar Kungiyar Hadin Kan Turai da ta kai ziyara a yankin na Gabas Ta Tsakiya, tun da kungiyar masu bin tsatsaurar ra’ayin islaman nan ta Hamas ta lashe zaben Majalisar Hukumar Falasdinawa, wanda aka gudanar a ranar larabar da ta wuce. A yau din ne dai kuma ta gana da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, inda ta bukace shi da ya angaza wa kungiyar Hamas din don ta amince da Isra’ila, kasar da a cikin manufofinta, kungiyar ta lashi takobin kau da ita daga doron kasa. Ta kuma nanata cewa muddin Hamas ba ta kwance damarar yaki ba, to Hukumar Falasdinawan za ta huskanci kasadar rashin samun taimakon kudi kuma daga kungiyar Hadin Kan Turai. Ita dai kungiyar ta EU, ita ce ta fi ba da taimako ga al’umman na Falasdinu.