Shugabar Brazil za ta gana da masu zanga-zanga | Labarai | DW | 22.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabar Brazil za ta gana da masu zanga-zanga

Dilma Rousseff ta yi alƙawarin soma tattaunwa da masu yin bore tare da ƙaddamar da sauye-sauye domin ingatan halin rayuwar al'umma.

Brazilian President Dilma Rousseff delivers a speech during a ceremony at Planalto Palace in Brasilia, on June 18, 2013. Rousseff said Tuesday that the voices of the hundreds of thousands of youths protesting across Brazil over the huge cost of hosting sporting events like the World Cup must be heard. AFP PHOTO / Evaristo SA (Photo credit should read EVARISTO SA/AFP/Getty Images)

Dilma Rousseff

Shugabar ta bayyana haka ne a wani jawabin da ta yi a daran jiya ta gidan talabijin da rediyo na ƙasar, tare da yin Allah wadai da yamutsin da ke faruwa:

Ta ce : ''Ya 'yan ƙasata Brazil ba za mu iya ci gaba da kasance wa cikin wannan hali na tashin hankali ba, wanda ka iya mayar da ƙarsarmu baya. Ta ce zamu yi amfani da ƙarfin doka ta kowane hali, domin yaƙi da kwasar ganima da fashi da jama'a ke yi a kan dukiyar gwamnati, domin yin hakan ya saɓama demokraɗiyya.''

Masu yin boren na kokawa ne da matsalar cin-hanci da ta zama ruwan dare da tsadar rayuwa da kuma maƙuden kuɗaɗen da ake kashewa, domin gina filayen wasan kwallon kafa. To amma shugabar ta kare shirin, kuma hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta ce ba za a fasa yin gasar kwallon kafa ta nahiyoyin da ake yi a ƙasar ba, da kuma ta duniya da za a yi a nan gaba.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman