Shugabannin wasu jamiyyu sun yi murabus a Birtaniya | Labarai | DW | 08.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabannin wasu jamiyyu sun yi murabus a Birtaniya

Shugaban jamiyar Liberal Democrate Nick Clegg da na wasu jamiyyun da suka fadi a zaben yan majalissa a Birtaniya sun yi murabus

A kasar Birtaniya Shugaban jamiyyar Liberal Democrat Nick Clegg ya yi murabus daga kan mukaminsa biyo bayan mummunan kayin da jamiyyarsa ta sha a zaben yan majalissar dokokin da ya gudana a kasar a ranar jiya alhamis.Ya bayyana yin murabus din nasa ne a lokacin wani taron manema labarai da ya kira a yau inda ya ce koda ya ke dama tun farko ya san da wanann zabe zai zamo masa mai matukar wahala to amma bai yi tsammahnin sakamakon zai zamo masa mummuna ba kamar yanda ya kasance.

Wanann dai shine kayi mafi muni da jamiyyar taLiberal Democrat ta sha tun bayan kafuwarta a shekara ta 1988.Har bayan karfe 11 na ranar yau dai jamiyyar ta Liberal Democrat wacce ke da kujeru 56 a majalissar da ta gabata ta samu kujeru 8 ne kawai a yayin da ya rage sakamakon zaben mazabu tara daga cikin 650.Jamiyyar yan konzavati ta fraministan kasar na yanzu dai ne David Cameroon ke a sahun gaba da kujeru 326 , wanda hakan ya bata isasshen rinjaye da zai bata damar jarorancin kasar a wani sabon waadin shekaru 5 ba tare da yin kawance da wata jamiyya ba.