Shugabannin Turai na taro ba Birtaniya | Labarai | DW | 29.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabannin Turai na taro ba Birtaniya

Ministar Scotland Nicola Sturgeon na halartar taron Tarayyar Turai a Brussels, taron da ke gudana a karon farko ba tare da bayyanar Birtaniya ba, sama da shekaru 40.


Taron na gudana ne a daidai lokacin da 'yan siyasar Birtaniyar ke cigaba da fafutukar maye gurbin Fraiminista David Cameron, wanda ya sanar da yin murabus biyo bayan kuri'ar raba gardamar da ta fitar da kasar daga Tarayyar Turan.

Sai dai ministar Scotland Nicola Sturgeon da ta ayyana manufar kasarta na ci gaba da damawa da EU, na cikin mahalarta taron na birnin Brussels da ya shiga rana ta biyu.

Shugaban gwamnatin Austriya Christian Kern ya ce dole ne dukkan bangarorin su san matsayinsu:

"Ya zamanto wajibi mu yi la'akari da cewar, akwai bangarori biyu a wannan tattaunawa. Hakan na nufin dole ayi la'akari da matsayin Birtaniya. Sai dai sanin kowa ne cewar, idan akwai sabuwar dangantaka da ta danganci 'yanci mai ma'ana, wajibi ne kuma wasu nauye nauye su biyo baya. Za mu tabbatar da hakan, ba za mu yarda da yarjejeniyar bangare daya kadai ba".

Shi kuwa shugaban EU Donald Tusk cewa ya yi, ana bukatar lokaci domin kura ta lafa kan wannan yanayi da Birtaniyar da ma kungiyar suka tsinci kansu ciki.