1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron share fagen ganawar shugabannin Koriya

Gazali Abdou Tasawa
August 13, 2018

Kasashen Koriya ta Kudu da ta Arewab sun tattauna kan shirya ganawa ta uku tsakanin shugaba Moon Jae-in da Kim Jong Un a watan gobe a ci gaba da kokarin sake farfado da dangataka tsakanin kasashen biyu. 

https://p.dw.com/p/33355
Kim Jong Un und Moon Jae In
Hoto: picture-alliance/dpa/Korea Summit press

 

A ganawar farko mai cike da tarihi da suka yi a watan Aprilun da ya gabata, shugabannin kasashen biyu sun cimma matsaya kan cewa Shugaba Moon ya soma da kai wa Shugaban Kim Jong Un ziyara a Pyongyang. 

Kawo yanzu dai ba kai ga tsayar da rana da kuma wurin da ganawa ta biyu ta shugabannin kasashen biyu za ta wakana ba. Tattaunawar share fagyen haduwar shugabannin kasashen biyu ta wannan Litinin za ta wakana ne a yankin Arewacin kauyen Panmunjom na kan iyayokokin kasashen biyu. 

A mako mai zuwa ne kuma Kasashen Koriyoyin biyu suka shirya za a yi ganawa ta farko a cikin shekaru uku tsakanin iyalai kasashen biyu wadanda yakin Koriya na daga 1950 zuwa 1953 ya raba da juna.