1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin EU sun gaza cimma daidaito kan mukamai

Abdul-raheem Hassan
June 21, 2019

Batutuwan muhalli da samar da ayyukan yi da makomar kungiyar ta EU na daga cikin manyan al‘amuran da suka mamaye taron shugabannin kungiyar.

https://p.dw.com/p/3KrHP
Belgien | EU Leaders' Summit in Brüssel
Hoto: picture-alliance/dpa/AA/D. Aydemir

Batun raba man'yan mukaman siyasa ne ya fi daukar hankali a jadawalin taron shugabannin na EU, ana kuma sa ran shugabannin su sa hannu kan matakin da ministocin kudi na kasashen da ke amfani da kudin Euro ya dauka a makon da ya gabata, wanda zai ba da damar bude kofa ga wasu shawarwari. Shugaban majalisar tarayyar Turai Donald Tusk ya yi tsokaci da cewa:

"Majalisar Turai ta yi tattaunawa ta musamman kan zaben tuntuba da batun da aka yi a majalisar tarayyar Turan. Babu wanda ya fi fifiko kan kowani dan takara. Majalisar Turai ta yadda cewa akwai bukatar shirin da zai yi dai dai da tsarin Tatrayyar Turai. Amma za mu sake haduwa ranar 30 ga watan Yuni."

Wani batu da ake cigaba da jayayya akansa, shi ne tsarin kasafin kudi na mambobi 19 na kasashen da ke amfani da kudin bai daya na euro, da ma makomar wadannan kasashe a nan gaba. Sai dai kasar Faransa ta riga ta gabatar da tsarin samar da asusun biliyoyin euro a wajen kasafin EU da zummar bunkasa zuba jari, tare da rage matsin tattalin arziki. Shugabannin majalisar kungiyar ta EU sun kuma tattauna matsalolin sauyin yanayi. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, a jawabinta ta nuna bukatar hadin kan kasashe mambobin EU na cimma yarjejenaiyar sauyian yanayi na Paris a 2015.

Yanzu dai jan aiki da ke gaban majalisar tarayyar Turan shi ne zaben sabon shugaba, ganin shugabannin majalisar sun gaza cimma matsaya kan wanda zai gaji Donald Tusk. Sai dai Merkel ta ce wajibi ne majalisar ta yi tsayin daka wajen cimma yarjejeniya don gudun baraka. Shugabannin kasashe mambobin kungiyar 28  na wata ganawar sirri a birnin Burussels, ana dai ganin ganawar na da alaka da tsayar da sabbin shugabanni, ko da yake kasashen Jamus da Faransa na ta kai ruwa rana kan magajin kujerar.