1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin Afirka sun tallata nahiyar a Davos

January 25, 2013

Shugabannin na Afirka na kokarin shawo kan masu zuba jari zuwa wannan nahiya sai dai rashin ingantattun hanoyin sadarwa da ababan more ruwa na kawo cikas.

https://p.dw.com/p/17RnP
Hoto: Reuters

Shugabannin kasashen Afirka da manyan 'yan siyasar wannan nahiya na daga cikin shugabannin duniya dake halartar taron tattalin arzikin duniya a Davos dake kasar Switzerland. Shugabannin na Afirka na kokarin shawo kan masu zuba jari zuwa wannan nahiya a saboda haka sun tallata kasashensu yadda ya kamata. Sun kuma tabo sanannun matsalolin da wannan nahiya ke fuskanta.

Shugabannin kasashen Guinea, Habasha, Najeriya, Ruwanda, Tanzaniya, Kenya da kuma Mauritius sun halarci wata liyafar cin abincin dare a wani otel dake Davos, inda suka tattauna game da makomar nahiyar Afirka musamman a fannin tattalin arziki. Wannan ganawar da aka yi ta a bayan fage yayin taron kan tattalin arzikin duniya an kuma gaiyaci manyan 'yan kasuwa da masu zuba jari.

Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma dake halartar taron na Davos ya yi kokarin kwantar da hankula dangane da tarzomar da ta auku a bara tsakanain ma'aikatan hako ma'adanai, wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane 50.

"Rikicin ya kau, mun hada kai da kungiyoyin kwadago da kamfanoni da gwamnati don tinkarar wannan lamari. Za mu daidaita al'amura. Bai kamata ya haifar da wani yanayi da zai zama mana gagarabadau ba."

A jerin kasashen Afirka kudu da Sahara, Najeriya ce kasa ta biyu bayan Afirka ta Kudu a karfin tattalin arziki. Kasar ta kwashe tsawon shekaru tana dogaro a kan man fetir inda ta yi watsi da aikin noma. Sai dai za a samu sauyi yanzu, domin Najeriya ta kaddamar da wani gagarumin shirin zuba jari da nufin sabunta fannin aikin nomanta. Maimakon kashe biliyoyin kudade don shigo da kayan abinci, Najeriya ta kuduri aniyar ciyar da kanta da kanta, watakila ma ta sayar da kayan abinci ga kasashen ketare nan gaba kadan. Ministan harkokin noma na Najeriya Akinwunmi Adesina bai yi wata rufa-rufa ba cewa ya je Davos ne don neman masu zuba jari.

Bildergalerie Angola Rohstoffe
Hoto: DW/R. Krieger

Jan hankalin kamfanonin ketare zuwa Afirka

"Hakika ina kokarin shawo kan masu zuba jari. Shugaban mu Goodluck Jonathan ya karbi bakoncin wani taro da ya samu halarcin shugabannin kamfanoni na kasa da kasa. Ni kai na tattauna da manyan kamfanonin noma. Suna son zuwa Najeriya domin sun gane damarmakin dake can. Idan ana maganar noma a Afirka ba kasar da ta fi Najeriya ."

A wasu fannonin ma masu zuba jari sun farga da damarmakin da nahiyar ta Afirka ke da su, musamman ma a fannin wayar salula. Suni Mittal shi ne shugaban kamfanin sadarwar na Bahrti a Indiya, kuma yanzu haka ya fadada kamfanin ya zuwa kasashe 17 na Afirka.

"Dukkan kasashen masu tasowa na samun bunkasa, nahiyar Afirka ce ke kan gaba. Daga cikin mutane miliyan dubu daya, rabinsu ba su da sabbin hanyoyin sadarwa. Wadanda ma ke da shin na son sun inganta zuwa intanet na tafi da gidanka. Wannan wata dama ce ga masu zuba jari irin mu."

Rashin abubuwan more ruwa

Babbar matsala ga ci gaban tattalin arzikin Afirka shi ne karancin hanyoyin sadarwa da ababan more ruwa kamar wutar lantarki da ruwan sha, sai kuma rashin hanyoyin sufuri dake kawo cikas ga harkokin cinikaiya, inji shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.

Bildergalerie Angola Rohstoffe
Hoto: DW/R. Krieger

"Afirka na da nakasu a fannin hanyoyin sadarwa. Shi ne ma ya sa ciniki tsakanin kasashen Afirka ya yi karanci. Aikewa da kaya daga Afirka zuwa Turai ya fi sauki idan aka kwatanta da tsakanin kasashen Afirka kansu."

Binciken ya nuna cewa dole a kashe akalla dala miliyan dubu 100 a shekara muddin ana son a inganta hanyoyin sadarwa a nahiyar ta Afirka. Sai dai abin mamaki duk da wannan matsala, kasashen Afirka da dama na samun bunkasar tattalin arziki fiye da kashi biyar cikin 100 a shekara.

Andreas Becker / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe

A kasa kuna iya sauraron karin rahotanni kan taron Davos.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani