Shugabannin ƙungiyar EU sun buɗe taron ƙoli a Lisbon | Labarai | DW | 18.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabannin ƙungiyar EU sun buɗe taron ƙoli a Lisbon

Shugabannin kasashen KTT EU sun fara wani taron kolin yini biyu a Lisbon babban birnin kasar Portugal don cimma yarjejeniya akan yiwa kungiyar gagarumin sauye sauye. Wannan yarjejeniya zata maye gurbin daftarin kundin tsarin mulkin EU wanda kasashen NL da Faransa suka yi fatali da shi a wata kuri´ar raba gardama da suka kada shekaru biyu da suka wuce. Shugabar hukumar EU Jose Manuel Barroso ya bayyana yarjejeniyar da ake sa ran cimma yana mai cewa.

Barroso:

“Sabuwar yarjejeniyar zata zama cikamakin muhawwarar da ake yi kan sake fasalin hukumomin EU kuma zata ba mu damar mayar da hankali kan sauye sauyen da ake samu a Turai da ma a duniya baki daya musamman a dangane da muhimman kalubale na hadakar manufofin duniya.”