1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabanni za su hadu a Burkina Faso

September 13, 2019

Shugabannin kasashen yammacin Afirka, za su yi wata ganawa a Burkina Faso a ranar Asabar, don sabunta dabarun yaki da ayyukan ta'addanci a kasashen yankin Sahel.

https://p.dw.com/p/3PWlo
Westafrikanische Präsidenten fordern zivile Regierung in Burkina Faso 05.11.2014
Hoto: AFP/Getty Images/I. Sanogo

Taron na yini guda wanda zai hada shugabannin kasashen da ke cikin kungiyar ECOWAS, zai kuma sami halartar shugabannin kasashen Kamaru da Chadi da ma na Moritaniya.

Shugabannin za kuma su yi bitar ayyukan rundunar tsaron nan ta G5 Sahel, da kasashen Burkina Faso da Chadi da Mali da Moritaniya da ma Nijar suka kaddamar a shekarar 2017.

Rundunar wacce aka tsara hada mata dakaru dubu biyar don tinkrarar matsalar tsaro a kasashen, ta fuskanci karancin kudade da ya rage hanzarin aikin yaki da mayakan tarzoma a yankin.

Ko a baya ma Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce da sauran gyara a yankin na Sahel.