Shugabanin Falasdinawa sun yi kiran samun zaman lafiya a yanki zirin Gaza | Siyasa | DW | 05.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shugabanin Falasdinawa sun yi kiran samun zaman lafiya a yanki zirin Gaza

P/M Palasdinawa Ismaila Haniya da shugaba Mahmoud sun yi kiran tsahirta fada a tsakanin magoya bayan su don dorewar zaman lafiya a yankin zirin Gaza.

Firaminista Ismaila Haniya na Falasdinawa

Firaminista Ismaila Haniya na Falasdinawa

A halin da ake ciki alámura sun lafa a yankin zirin Gaza bayan kiran da shugabannin ɓangarorin Hamas da fatah suka yi ga mabiyan su domin kawo ƙarshen tarzomar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane goma sha daya a kwanaki biyun da suka gabata.

Bayan wata tattaunawa da ta gudana a talatainin dare tsakanin shugaba Mahmoud Abbas da P/M Ismaila Haniya, shugabannin biyu sun yi kira ga magoya bayan su, su kaucewa dukkan wata fitina tare kuma da buƙatar sojojin sa kai su janye daga dukkanin tituna, a dai halin da ake ciki an jibge yan sanda a koina a faɗin yankin domin tabbatar da doka da oda. A waje guda kuma P/M Ismaila Haniya yace zai kafa kwamitin bincike ƙarƙashin jagorancin wani alƙali domin duba rikicin da ya ɓarke na baya bayan nan a tsakanin Palasdinawa.

An sami ƙaruwar faɗace faɗace a yankin zirin Gaza da kuma gaɓar yamma, tun bayan da shugaba Abbas ya yi kiran gudanar da zaɓen majalisun dokoki dana shugaban ƙasa tun gabanin cikar waádi bayan da tattaunarwar kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa a tsakanin ɓangarorin biyu ta ci tura.

A can baya dai irin wadannan yarjeniyoyi sun sha cin karo da tarzoma da tashe tashen hankula, Alumar yankin Gaza na baiyana damuwa a game da abin da zai biyo bayan janaizar waɗanda suka rasu a tarzomar ta ranar Alhamis. A wani mataki da ka iya tayar da hankula, Amurka ta sanar da cewa zata bada gudunmawar dala miliyan 86 domin karfafa rundunar tsaro dake goyon bayan Mahmoud Abbas wanda zai faɗada shigar Amurka cikin yunkurin da Fatah ke yi da jamiyar Hamas a gwagwarmayar madafan ikon.

A faɗan da ya faru a Gaza a ranar Alhamis, tsakanin ƙungiyoyin biyu na Palasdinawa masu hamaiya da juna, wasu yan bindiga daɗi na jamíyar Fatah sun bindige wani ɗan sanda dake goyon bayan ɓangaren Hamas na Ismaila Haniya. Harbin wanda Hamas suka alhakin sa a kan Kanar Mohammed Ghareeb na rundunar ko ta kwana, a matakin maida martani, sojin sa kai na Hamas suka yiwa gidan kanar din dake Beit Lahiya ƙawanya inda suka bindige shi har lahira tare da wasu muƙarraban sa su shida da kuma jiwa matar sa rauni. Bugu da ƙari an sami ɓarkewar wasu tashe tashe hankulan a kusa da sansanin yan gudun hijira na jabaliya wanda ya jikata a ƙalla mutane 30. faɗan ya kuma bazu ya zuwa yankin gaɓar yamma inda wasu yan bindiga daɗi da baá san ko su wanene ba suka jikata wani ɗan Hamas a garin Nablus. A bangare guda kuma sojin Israila sun kai farmaki garin Tulkarm dake kusa da gaɓar yamma a cigaba da abin da suka ce farautar wani ɗan takife na ƙungiyar Jihadil Islami.