Shugabani nawa suka jagoranci Amirka? | Amsoshin takardunku | DW | 12.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Shugabani nawa suka jagoranci Amirka?

Shugabanin Amirka ɗaya bayan ɗaya tun daga George Washington har zuwa Barack Obama.

President-elect Barack Obama is welcomed by President George W. Bush for a meeting at the White House in Washington, Wednesday, Jan. 7, 2009, with former presidents, from left, George H.W. Bush, Bill Clinton, and Jimmy Carter. (AP Photo/J. Scott Applewhite)

Obama da tsafin shugabanin Amirka huɗu

Daya na bin ɗaya Amurika ta samu shugabanin ƙasashe 43 har da shugaban mai ci yanzu wato Barack Obama, wasu na cewa 44 saboda akwai shugaban da bayan an zaɓe shi ya gama wa'adin mulkinsa kuma bayan wasu shekaru ya sake dawowa aka kuma zaɓe shi.

Shugaban Amurika na farko bayan da ƙasar ta samu 'yancin kanta, daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya shine shugaba George Washington wanda shine ya jagorancin ƙwatar mulki daga turawan mulkin mallaka.Ya samu karɓuwa sosai daga Amurikawa ba shi da jam'iya siyasa saboda haka, so biyu ana zaɓen ba tare da hamaya ba,kuma ya samu ƙuri'u dari bisa dari.

New York - George Washington Memorial 25695197_babimu - Fotolia 2010

George Washington

George Washington yayi mulkin Amirka daga 1789 zuwa 1797. Na biyu shine John Adams wanda ke matsayin mataimakin shugaban ƙasa zamanin mulkin George Washington, ya yi mulkin Amirka daga 1797 zuwa 1801.

Shugaba na ukku shine Thomas Jefferson shima jigo ne daga mazan da suka ƙwatarawa Amirka 'yancin.Shi ya rubuta sanarwar samun 'yanci.Ya riƙe matsayin mataimakin shugaban ƙasa zamanin mulkin Adams.Shi ya hito daga jam'iyar Republican -Democtare.Yayi shekaru Takwas kan kujera mulki daga 1801 zuwa 1809.

Shugaban Amirka na huɗu sunansa James Madison na jam'iyar Republicabn -Democrate, shima ya yi shekaru Takwas kan mulki.Shugaba na biyar shine James More wanda shima yayi shekaru Takwas daga jam'iyar Republican-Democrate.Shugaba na shida sunansa John Q.Adams ,wato ɗan shugaba na biyu.Shi ma ya yi mulki taswan shekaru huɗu.Ya hito daga jam'iyar Republican National.

Shugaban Amurika na bakwai sunansa Andrew Jackson, ya hito daga jam'iyar Democrate.Sai kuma mai bi masa mai suna Martin Van Buren wanda ya mulki Amirka daga 1837 zuwa 1841 daga jam'iyar Democrate.Sai shugaba na Tara mai suna Wiliam H.Harrison daga wata jam'iya mai suna Whig.Saidai shi wata ɗaya kacal yayi kan karagar mulki.Ya rasu sanadiyar rashin lafiya.

Wanda ya gaje sa sunana sa John Tyler wato shugaba na 10 kenan shima yayi shekaru huɗu.

Shugaban Amirka na 11 sunansa James K.Polk na jam'iyar Democrate.Sai kuma mai bi masa Zachary Taylor shima na jam'iyar Whig.Ya rasu bayan ya yi watani16 kan karagar mulki.

Daga nan sai Millard Fillmore shima na jam'iyar Whig,ya gaje shi.

An shirya zaɓen na gaba shekara 1853 inda Franklin Pierce na jam'iyar Democrate ya lashe kuma yayi shekaru huɗu kan karagar mulki.

A zamanin mulkinsa aka girka jam'iyar Republican ta yanzu.

Shugaba na 15 shine James Buchanan na jam'iyar Democrate shima ya yi shekaru huɗu kan kujera mulki.

FILE -In this Oct. 1858 file photo, President Abraham Lincoln is shown in a photograph by W.A. Thomson, made in Monmouth, Ill., on the day of his debate with Stephen A. Douglas. (ddp images/AP Photo/W.A. Thomson)

Abraham Lincoln

Daga shi sai Abraham Lincoln, wanda shine shugaba na farko da ya fito daga jam'iyar Republican.A lokacin sa ne Amirka ta soke dokar cinikin bayi.An zaɓe shi wa'adin mulkin na biyu amma bai ida ba wani mutum mai suna John Wilkes Booth ya kashe shi a birnin Washington.

Wanda ya gaje shi shine Andrew Jonson na Democrate, wanda shima yayi shekaru huɗu kan karagar mulki Amirka.

Sai shugaba na 18 mai suna Ulysses S.Grant na Republican,wanda lokacinsa ne aka ƙaddamar da dokar da ke ba bayi baƙar fata 'yanci ta fannin siyasa.

A shekara 1877 an zaɓi shugaba na 19 wato Rutherford B. Hayes shima na jam'iyar Republican.Sai kuma shugaba na 20 mai suna James A. Garfield wanda bayan watani shida aka kashe shi.

Wanda ya gaje sa shima ya hito daga jam'iyar Republican, sunansa Chester A.Arthur yayi mulki har zuwa shekara 1885.Bayan sa aka zaɓi shugaba na 22 wani mai suna S.Grover Cleveland na jam'iyar Democrate, kamin jam'iyar Republican ta ƙwace mulki a shekara 1889 inda ta dora Benjamin Harrison.Bayan shi aka sake zaben S.Grover Cleveland wato shugaban Amirka na 22, ya zama kuma shine na 24.

William Mckinly na jam'iyar Repubilan ya gaje shi a shekara 1897, bai ida wa'adin mulkinsa aka kashe shi.

Kamin mu kai ga shugaba na 26 sai mu ɗan sarara.

Shugaban Amirka na 26 shine Theodore Roosvelt ɗan Republican yayi mulki daga 1901 zuwa 1909.Willam H.Taft ya gaje shi shima na Republican, inda yayi wa'adin mulkin shekaru huɗu.

President Truman sits before a microphone, holding his speech, at the White House, Washington, DC, May 8, 1945, after he had finished reading his announcement to the nation that Allied Armies have won unconditional surrender from the German forces on all fronts. (AP Photo/stf)

H. Truman

Daga 'yan Democrate suka ƙwace mullki su dora T.Woodrow Wilson, yayi mulki har tsawan Takwas.A zamanin mulkinsa ne mata suka samu 'yancin kaɗa kuri'a a Amirka, sannan daga cikin shika-shikan da suka girka Majalisar Dinkin Duniya ta farko, bayan yakin duniya na farko.

Shugaban Amurika na 29 shine Warren G.Harding daga jam'iyar Republican, ya mulki daga 1921 zuwa 1923, ya rasu a yayin da ya shiga shekara ta ukku ta wa'adin mulkinsa.

Bayan ya mutu sai mataimakinsa J.Calvin Coolidge ya gaje shi.Ya cika shekara guda na wa'adin marigayin sannan kuma a ka zaɓe shi a saban wa'adi na shekaru huɗu.

Sai Herbert C.Hoover ya zama shugaba na 31.

Der republikanische Präsidentschaftskandidat Richard Nixon (l) und sein demokratischer Kontrahent John F. Kennedy reichen sich nach ihrem Fernsehduell in New York am 21.10.1960 die Hände. Das vierte und vermutlich letzte TV-Rededuell der beiden amerikanischen Präsidentschaftskandiaten endete mit einer klaren Überlegenheit Kennedys. +++(c) dpa - Report+++

J. F.Kennedy da Nixon

Shugaban Amirka na 32 shine Franklin Delano Roosvelt, na jam'iyar Democrate.A zamanin mulkinsa ne a ka yi yaƙin duniya na biyu.Yayi jagorancin Amurika tsawan shekaru 12 daga 1933 zuwa 1945.Amurika na ɗaukar sa a matsayin shugaba na uku ta fannin farin jini daga jam'a, wato bayan Abraham Lincoln da George washington.Franklin Delano Roosvelt shione shugabvan Amurika wanda ya aka taba zaba har sau hudu jera-jerai.Bai ida wa'adin mulkinsa ba, ya rasu ranar 12 ga watan Afrilu na shekara 1945, wato wata guda kacal kamin ƙasashe abokan ƙawancen Amurika su ci yaƙin duniya na biyu.

Bayan Roosvelt sai mataimakinsa Harry S.Truman ya hau karagar mulkin Amurika, domin ya ida wa'adin mulkin marigayin kamin a zaɓe shi a shekara 1953.A jimilce ya mulki Amurika tsawan shekaru Takwas.A lokacin mulkinsa ya bada umurnin harba makaman ƙare dangi a biranen Hiroshima da Nagazaki na ƙasar Japan, wanda suka haddasa mummunan tadi m, kuma suka zo ƙarshen yaƙin duniya na biyu.

Sai shugaba na 34 wato Dwight D: Eisenhower wanda ya taka burki ga mulkin shekrau 20 na jam'iyar Demnocrate.Shima kuma ya jagorancin Amurika tsawan shekaru Takwas daga 1953 zuwa 1961.A zamanin mulkinsa ne Amirka ta ƙirƙiro hukumar NASA mai binciken sararin samaniya.

Daga shi sai shugaba John F.Kennedy dan Democrate, yayi mulkin tsawan shekaru biyu kacal, kamin wani mutum ya bindige shi ranar 22 ga watan Nowemaba na shekara 1963 a yainda ya ke cikin shekaru 46 da aihuwa.Shugaba Kennedy ya bar tarihi kwarai , misali a jamhuriya Nijar inda har yanzu akwai gada da ya gina mai suna Pont Kennedy wadda ta haɗa birnin Yamai da bayan ruwa ko kuma Haro Banda.

Bayan kisan shugaba Kennedy, sai mataimakinsa mai suna Lyndon B.Johnson ya dauƙi ragamar shugabanin Amirka, ya jagoranci har zuwa shekara 1969.

** FILE ** President Ronald Reagan gives a thumbs-up to supporters at the Century Plaza Hotel in Los Angeles as he celebrates his re-election, Nov. 6, 1984, with first lady Nancy Reagan at his side. Reagan's win over Walter Mondale, 525 to 13 in the electoral vote and 59 percent to 41 percent in popular votes, was unquestionably a landslide election. (AP Photo/File)

Ronald Reagan

Daga nan sai Richard M. Nixon dan jam'iyar Republican,ya zama shugaban ƙasar Amirka.Yayi murabus daga muƙaminsa a shekara 1974 sakamakon matsin ƙaimi da ya fuskanta game da zarginsa da kayi da hannu a cikin wata baddaƙalla da aka raɗawa suna Watergate

inda aka ce yayi amfani da muƙaminsa domin yin katsalandan cikin harkokin shari'a.Wata ɗaya bayan murabus ɗin sai mataimaƙain sa Gerald R.Ford shima ɗan Republican ya ci gaba da mulki.Shine shugaban Amirka wanda ba a taɓa zaɓe ba, domin ya hau mulki sakamakon murabus ɗin da Nixon yayi, sannan da ya ajje takara a shekara 1976, bayan ya kammala wa'adin mulkin mariganyi Nixon sai kuma ɗan takara Democrates James E. Jimmy Carter ya kada shi.Saboda haka Jimmy Carter ya zama shugaban Amirka na 39.

Ya yi mulkin Amirka har zuwa shekara 1981.

Wanda ya gaje shi shine shugaba Ronald Reagan na jam'iyar Republican , yayi mulkin shekaru Takwas har zuwa shekara 1989.

Source News Feed: EMEA Picture Service ,Germany Picture Service U.S. President Barack Obama delivers a statement on the U.S. Fiscal Cliff in the East Room of the White House in Washington, November 9, 2012. REUTERS/Jason Reed (UNITED STATES - Tags: POLITICS BUSINESS)

B.Obama

Sai shugaba na 41 wato George W.Bush shima ɗan Republican, wanda yayi shekaru huɗu ya na mulki.daga shi sai William Bill Clinton na Democrate, wanda yai jagoranci daga 1993 zuwa shekara ta 2001.Shima shugaba ne wanda ya samu karɓuwa ƙwarai daga Amirka.

George W.Bush dan shugaban Bush na 41 ya gaji Clinton a shekara 2001 har zuwa shekara ta 2009, inda shugaba mai ci yanzu Barack Obama ya hau gadan mulkin Amiria a matsayin baƙar fata na farko.Bayan ya kamalla shekaru huɗu nan farko a sake zaɓen shi a wa'adi na biyu ranar shida ga watan Nowemba na shekara 2012.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu