1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Kagame zai sauka daga mukamin shugabancin AU

Zulaiha Abubakar
February 10, 2019

Shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame zai sauka daga mukamin jagorancin kungiyar tarayyar Afirka yayin da shugaba Abdel Fattah al-Sisi na kasar Masar zai maye gurbinsa yayin taron kungiyar AU da ke gudana kasar Habasha.

https://p.dw.com/p/3D4fO
Äthiopien Addis Abeba Außenminister vor dem Treffen der Afrikanischen Union
Hoto: picture-alliance/AA/M. W. Hailu

Jagorancin kungiyar na zagayawa ne tsakanin yankuna biyar na nahiyar Afirka, batun yawaitar rikice-rikice ne kan gaba cikin batutuwan da shugabannin kasashe 55 na kungiyar za su tattauna, da yake jawabi kafin taron babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya baiyana zabubbukan da suka gudana a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Mali da kuma Madagaska a matsayin abin a yaba, ya kuma kara da cewar a yanzu Afirka ta fara zama abin misali ga sauran kasashe sakamakon irin yadda aka samu ingantuwar alaka tsakanin kasashen Habasha da Eritiriya da Sudan ta Kudu da kuma  Afirka ta tsakiya.